Monday, April 1, 2019

KIRAN DA KUNGIYAR KIRISTOCIN NIGERIA TAYI GA MAJALISUN WAKILAI DA DATTAWA

Kungiyar kiristocin Nigeria wadda aka fi sani da suna CAN tayi kira da a zabi mabiyin addinin kirista a matsayin shugaban majalisar dattawa ko kuma shugaban majalisar wakilai. A cewar su hakan zai nuna cewa anyi raba-daidai a tsakanin manyan addinan na Nigeria.
Sanarwar wadda ta fito daga bakin Pastor Adebayo Oladeji, mataimaki na musamman akan harkokin yada labarai ga Reverend (DR) Samson Ayokunle shugaban kungiyar ta CAN a ranar Litinin 1 ga watan Afrilu 2019. A cewarsa da shugaban kasa da chif jojin kasar dukkansu musulmai ne.
Ga kadan daga abinda sanarwar ta kunsa “kamar yadda kuke shirye-shiryen zabar shugabannin majalisa, kungiyar CAN tana kira gare ku da kuyi raba-daidai a wajen rabon manyan mukamai don kaucewa wariya.
Mu yayan kungiyar kiristocin kasar nan mun san muhimmancin majalisun dokoki da kuma rawar da suke takawa ta bangaren zaman lumana da cigaban kasa a siyasance. Saboda haka muna kira da ayi raba-daidai a tsakanin addinai da kabilu a wajen zaben shugabannin wadannan majalisu masu girma.
Koda yake muna sane cewa majalisar dattawa da wakilai suna da manyan mukamai da yawa amma mu abinda muka fi mayar da hankali akan shi shine shugabancin majalisun.
Kamar yadda aka saba tun shekarar 1999 duk lokacin da shugaban majalisar dattawa ya kasance kirista to shugaban majalisar wakilai zai kasance musulmi ne. kuma haka yake ko a wajen zaben mataimakan shugabannin…..”
Hakanan kuma kungiyar tayi ga majalisun akan su kasance masu adalci ga kowa da kowa ba tare da amfani da bangaranci ko bambancin addini ba.
Previous Post
Next Post
Related Posts

0 comments: