Da yawan ƴan matan da suke jefa kansu a cikin wannan ƙazamar harka, suna yinta ne don ciyarwa da tufatar da kansu.
Wannan ne dalilin da yasa kamfanin dillancin labarai na BBC ta yi hira da wasu ƴan mata mazauna ƙasar wato Mariam da Fatmata sun bayyana yadda ake saduwa da su a tsawon kwana daya inda ake ba su Leone 5,000 wato kimanin naira 180 na kudin Najeriya.
Fatmata Kanu ta bayyana cewa mafi yawan jima'in da ake yi da ita ba ta hanyar amfani da kwaroron roba bane. Hakan kuwa yana faruwa ne kasancewar tsadar da kwaroron roba din yake da ita a ƙasar.
Mariam ta bayyana cewa tana da ƙanne biyu waɗanda itace take kula da cin su, suturar su da kuma kudin makarantar su.
0 comments: