Monday, April 1, 2019

SHUGABA BUHARI YAYI BALAGURO ZUWA SENEGAL

Yanzu haka shugaba Muhammadu Buhari yana bisa hanyar shi ta zuwa Senegal, don halartar taron rantsar da takwaransa na Senegal wato Macky Sall.

Shugaban dai ya halarci taron ne bisa amsa gayyatar da aka yi masa, a matsayin sa na shugaban kungiyar ECOWAS kuma dai harwayau shine bako na musamman a taron. Za'a gabatar da taron ne a Diamniadio Exhibition Centre a gobe Talata 2 ga watan Afrilu, 2019.

Shugaba Muhammadu Buhari ya samu rakiyar gwamnonin jahohin Nasarawa, Bauchi da Kaduna wato Muhammadu Abubakar, Nasiru El-Rufa'i da Tanko Al-Makura.

Sauran yan rakiyar sun hada da ministan harkokin kasashen ketare Mr Geoffrey Onyeama, mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Maj-Gen Babagana Monguno (rtd) Ambassador Ahmad Rufa'i da sauransu.

Ana sa ran shugaban zai dawo da zaran an kammala rantsuwar.
Previous Post
Next Post
Related Posts

0 comments: