Monday, August 19, 2019

WANI MUTUM YA WATSAWA MATARSA DA ƳAƳANSA ACID A KATSINA


Wani mutum wanda har yanzu ba'a tabbatar da sunansa ba ya watsawa matarsa da ƴaƴansa acid a lokacin da suke bacci.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ɗandume dake jahar Katsina.

Mutumin dai ma'aikaci ne a Union Bank reshen karamar hukumar dake jahar. Har ya zuwa yanzu dai ba'a san dalilin mutumin na aikata wannan danyen aiki ba.

Yanzu haka dai ba'a san inda mutumin ya ɓuya ba, sai dai Rabi wato matar da ƴaƴan nasa an garzaya dasu zuwa asibitin koyarwa ta Jami'ar Ahmadu Bello dake shika don ceto rayuwar su.


Previous Post
Next Post
Related Posts

0 comments: