Saturday, August 3, 2019

YADDA KANEN MIJINA YAYI JIMA'I DA NI INA ZATON MIJINA NE



Madam Ajayi mai kimanin shekaru hansin da biyu ta bayyana wa kotu yadda kanen mijinta yayi basaja har ta amince tayi kwanciyar jimai da shi,  alhali tana zaton mijinta ne. Madam Ajayi ta bayyana hakan ne a gaban kotu bayan da mijin nata ya kai karar ta a gaban kuliya bisa zarginta da yake yi da bin maza. Da wannan dalilin ne mijin ya bukaci kotu da ta shiga tsakani ta hanayar raba auren nasu duk da kasancewar sun shafe shekaru sama da talatin a matsayin miji da mata tare samun albarkar yara hudu a tsakaninsu.

Madan Ajayi ta bukaci kotu da ta yi watsi da bukatar mijin nata saboda a cewarta ita tana son mijin nata.

Matar ta bayyana cewa yadda abin ya faru "mijina ya kama mani hayar gidan da nake zaune, wata rana sai ga kanensa yazo gidan da misalin karfe tara na dare wanda wannan lokacin ne mijina ya saba zo man, bai yi wata-wata ba sai fara wasa da ni har yayi jima'i da ni sai bayan da ya gama ne na gane ashe ba mijina bane. Abin ya dame ni sosai, wannan ne dalilin da yasa na bayyana ma matar yayana inda ta shawarce ni da nayi shiru da bakina don hakan na iya jaza rikici a tsakanin yan uwan.

A nasa bangaren, mijin yace yana da wasu matan bayan ita kuma baya son hada su zama a gida daya hakan yasa ya kama mata haya sai dai tun bayan da ya kama ma matar tasa haya, labarai ke zuwa masa marasa dadin ji game da matar, sai dai bai taba kulawa ba. Amma yanzu ya samu yakinin matar tasa tana bin maza, don haka yake bukatar kotu data raba auren nasu.

Kotu ta daga karar zuwa 22 ga watan Agutan wannan shekarar don cigaba da sauraron karar, sai dai alkalin ya shawarci ma'auratan da suyi koarin sulhu a tsakanin su.
Previous Post
Next Post
Related Posts

0 comments: