KOTU TA AMINCE DA FITAR ZAKZAKY ZUWA KASAR INDIYA DON DUBA LAFIYAR SHI
Kotu ta amince da bukatar lauyoyin kungiyar Islamic Movement Of Nigeria (IMN) na fita ƙasashen ketare don duba lafiyar shi.
Kotun ta amince da fitar shi zuwa ƙasar Indiya shi da matar shi Hajiya Zeenatu Ibrahim Zakzaky.
Idan ba'a manta ba dai sojoji ne suka harbi Zakzakyn shi da mai dakin sa tun shekarar 2015. Wanda hakan ya faru ne sakamakon wata hatsaniya data barke tsakanin mabiya shi'a Zakzakiyya da sojojin.
Kotun tayi amince da zuwan su asibitin Mandeta dake da matsuguni a birnin New Delhi dake ƙasar ta indiya.
0 comments: