Saturday, August 3, 2019

WANDA ZAI GAJE NI A SHEKARAR 2023



Shugaban kasa Muhammadu Buahari ya bayyana matsayinsa akan wanda zai gaje shi bayan wa'adinsa ya kare a shekarar 2023. shugaban yayi bayanin ne a lokacin da wata kungiya mai suna ‘Progressibe in Academics’ (Pro-Acad) a fadar shugaban kasa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Shugaban ya bayyana cewa lallai ba zai bayyana wanda zai gaje shi a matsayin shugaban kasa ba bayan karewar wa'adinsa a shekarar 2023, saboda matsaloli da gutsiri tsoma da hakan ka iya haifarwa. Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da mambobin kungiyar suka bukaci da ya fara shirye-shiryen koyar da wanda zai gaje shi al'amuran shugabanci.

Shugaban ya kuma bayyana cewa kada ya sanya ma ransa samun kujerar cikin ruwan sanyi, kasancewar samun kujerar shugaban kasa yana bukatar aiki tukuru, hakuri da kuma dagewa. Anan ya bayar da misali da kansa irin yadda ya dade yana hankoron samun kujerar tun shekarar 2003 amma hakarsa bata cimma ruwa ba sai a shekarar 2015. 
Previous Post
Next Post
Related Posts

0 comments: