Saturday, August 17, 2019

LABARIN SARKI MAI MATA HUDU


Anyi wani shahararren sarki wanda yake da matan aure guda hudu.

Yana matukar matarshi ta huɗu wato amarya, yana ji da ita kamar ya haɗiye ta saboda tsabar soyayya. Komai zai mata baya son ƙarami ko mai araha.

Hakanan kuma yana mugun son matar shi ta uku wato mai bi ma amarya. Itace matar da ake nuna wa sarakunan duniya saboda ya fi alfahari da ita akan kowace.

Harwayau kuma yana son matar shi ta uku wato mai bi ma uwar gida saboda mutunci da hakurin ta.

Duk sa'adda sarki yake cikin damuwa da ita yake shawara kuma cikin ikon Allah sai ta kwaranye ma sarki damuwar shi

Sai matar shi ta farko, ita kuma tafi sauran kirki da ladabi da biyayya, da bayar da gudunmuwa wajen kula da dukiyar sarki da masarautarsa amma kuma sarki baya kaunar ta ko kaɗan. Koda yake tana matukar kaunar sarki amma hakan bai taɓa sanyawa ya kula da ita ko ya damu da sanin halin da take ciki ba.

Ana nan akan haka, wata rana sai ciwon ajali ya kama sarki. Da dai ya kura cewa ba zai kai labari ba sai ya kirawo duka matansa guda huɗu. Suka zo suka durkusa a gabansa

Ya dubi amarya yace "amarya ki tuna ina nafi kaunar ki akan dukkan matana, ko sutura bakya sanyawa sai mai tsada, ina baki kulawa fiye da dukkan matana, gashi yanzu ina shirin mutuwa na bar duniyar shin zaki raka ni?

Amarya tace "gaskiya ranka ya dade wannan ba zata taba saɓuwa ba wai bindiga a ruwa" bata kara cewa komai ba ta fice ta bar musu ɗakin.

Sarki yaji ciwon maganar da tayi don sai da yaji tamkar yankan wuka a zuciyar shi. A haka ya daure ya waiwayo zuwa ga mai bi ma amarya yace: "ina son ki ina kaunar ki gashi mutuwa zata raba mu shin zaki bini mu tafi tare?"

Matar ta amsa tace "a'a bazan bika ba, wannan rayuwa mai dadi idan ka mutu ma wani zan sake aure."

Ran sarki ya kara ɓaci, ya daure ya juyo zuwa ga mata ta uku yace: "koda yaushe nake cikin damuwa kece kike yaye man, kina karfafa man gwiwa ta bangarori da dama a rayuwar duniya gashi zan tafi na bar ki, shin zaki biyo ni mu tafi tare?"

Mata ta uku tace: "gaskiya ranka ya dade kayi hakuri bazan iya taimaka maka a wannnan lokacin ba, iya abinda zan iya yi shine zan raka ka har kabarin ka, daga nan na dawo kai kuma kayi gaba"

Ran sarki ya ɓaci, ya dugunzuma ya rasa abinda yake masa daɗi. Kwatsam sai yaji muryar uwargida tana cewa "ni zan bika mu tafi tare duk inda zaka je"

Sarki ya cika da mamaki da nadama, yana faɗa a zuciyar shi cewa ina ma nasan kece kika fi kauna ta na kyautata maki, ina ma ban cutar dake ba, ina ma ace ban banzatar dake na fifita sauran matana akan ki ba.

DARASI
Idan ka dubi rayuwar mu, dukkan mu kowa yana da mata hudu kamar wannan sarkin.

Mata ta huɗu wato amarya itace jikin mu, duk yadda kake kawata shi da ado da kulawa dole zai bar mu idan muka mutu.

Mata ta uku itace dukiya mukami dole idan muka mutu ya tashi daga kan mu ya koma kan wani.

Mata ta biyu sune ƴan uwan mu da abokan arziki duk yadda suke son taimakon mu da bamu shawara da zaran mun mutu iyakar su kabarin mu daga zasu yi kwana su bar mu a can.

Mata ta huɗu itace ruhin mu wanda muke shagaltuwa da rashin kula shi saboda kwadayin abin duniya. Alhali ruhin mu ne kawai zai kasance a tare da mu duk inda muka shiga.

Shuka alkhairi a rayuwa don cin ribar ka duniya da lahira, idan kayi wasa da damar ka ta lokaci da Allah ya baka zaka kasance cikin masu nadama kamar yadda sarki yayi nadamar rashin kula matarsa ta huɗu.

Domin cigaba da samun rubuce-rubucen mu ba tare da ka ziyarci shafin mu ba a danna alamar allow ko kuma a sanya email a yi subscribing din shafin mu.
Previous Post
Next Post
Related Posts

0 comments: