MU YI NISHADI
Wai wata amarya ce take zaune da angonta suna hira, irin
hirar nan ta sabon aure. Kwatsam! Sai mijin shauki ya kwashe shi yayi subul da
baki, yace: “my love wai ina wannan kawar taki?”
Sai matar tace: “wacece kenan?”
Sai yace: “haba my
love baki gane ta wata fara doguwa, gata da hanci, gata da manyan idanuwa, ga
hakoranta farare tamkar hasken fari wata, ga iya kwalliya gaskiya kyakkyawace
sosai” Nan take ran amarya ya.
Sai tace ai jiya muna tare da ita mijinta yazo ya dauketa,
gaskiya mijin nata ya bala’in haduwa, ga shi fari gashi dogo, ga saje gaskiya
nayi rashi wallahi domin shine irin mijin da naso na aura ban samu ba sai Allah
ya hada ni da kai.
Amarya bata karasa kai aya ba, sai ta ji saukar mari a
fuskarta, ji kake tasssssss!!!
Wai idan kece yaya zaki yi?
0 comments: