Sunday, March 31, 2019

ABIN TAUSAYIN DA YA FARU DA WANI BAWAN ALLAH, MUTANE AYI HATTARA


Wasu mutane su uku suka je wurin da ake sayar da mota suka yi cinikin mota kirar Toyota Camry 2013 akan kudi naira miliyan 5. Bayan an karkare ciniki sai suka bukaci mai sayar da motocin da ya basu account details dinsa na banki, mutumin bai yi gardama ba ya basu account number da sauran details din da suka bukata saboda bai kawo ma ransa faruwar wani abu ba.

Kwana uku bayan karbar bank details sai suka yi ma mai sayar da motocin transfer na miliyan uku. Jim kadan bayan tura kudin sai ga mutanen sun zo wajen mai sayar da mota suka bashi hakurin cewa sun buga sun buga basu samu halin cikon milyan biyu din ba, amma mutumin yayi hakuri ya basu miliyan biyu da rabi (2.5 m) shi kuma ya dauki ₦500,000.

Mai sayar da motoci yayi farinciki da jin haka ganin ko cika kudin suka yi ba lallai ne ya samu ribar ₦500,000 ba, ballantana ga motar shi ga kuma kyautar 500,00 ba tare da yayi aikin fari ballantana na baki ba. Bai tsaya bata lokaci ba ya kawo kudi 2.5 million ya bayar. Su kuma mutane suka yi tafiyar su.
Bayan kwana uku da faruwar lamarin, kwatsam sai gungun yan sanda masu yaki da garkuwa da mutane da aka fi sani da Anti kidnapping squad suka yi ram da mai sayar da motoci a bisa zargin shi da laifin garkuwa da mutane.
Ashe wadannan mutanen masu garkuwa da mutane ne, sun yaudare shi sun amshi account details dinsa ne don su karbi kudi daga hannun victim dinsu, yanzu su sun fece da kudi sun bar mai sayar da motoci cikin cakwakiya.
Previous Post
Next Post
Related Posts

0 comments: