SHUGABANNIN DA MUKA RASA IRIN SU A YAU
A shekarar 1963 wani dan jaridar ingila yazo Lagos babban birnin tarayya a wancan lokacin don tattaunawa da firayim minister Sir Abubakar Tafawa Balewa. Sai aka sanar da shi cewa ya tafi hutun shekara (annual leave) sai ya tambaya wace kasa ya tafi, aka bashi amsa ya tafi kauyensu ne hanyar jirgin kasa. Baturen ya cika da mamakin jin wai shugaban kasa a jirgin kasa kuma wai ya tafi hutu a kauyen su. Don haka bai yi wata-wata ba ya tafi Bauchi don ganewa idonsa. Bai zame ko ina ba sai Tafawa Balewa.
Isar shi garin ke da wuya, sai ya kara cika da mamaki don bai ga alamar firayim minister yana garin ba, bai ga tarin motoci ba, bai ga yawan zirga zirgar jami’an tsaro ba, bai kuma ji koda jiniya alamar akwai wani muhimmin mutum a cikin garin ba, shi dai ya ga kowa ya shagaltu da aikin gabansa.
A hanya sai ya hadu da wani manomi yana dawowa daga fadama ya debo rake akan jakinsa, sai ya tambayi manomin inda zai iya haduwa da firayin minister. Baturen ya kara cika da, mamaki lokacin da manomin yake bashi labarin cewa yanzun nan ya wuce shi zaune a kofar gida shi da jikokin shi, har ma yayi masu kyautar rake.
A haka kuwa dan jaridar ya same su kamar yadda wannan mutumin ya bayyana masa, ba tare da bata lokaci ba yayi masu wannan hoton. #HistoryVille
0 comments: