Tuesday, February 15, 2022

Karatun tafin hannu

 

Join the Google Web Creators community! Complementing the community forums, you’ll now get Blogger news, general blogging tips & inspiration, product updates from Google via Google Web Creators. Follow us on Twitter, Instagram, YouTube, or our blog to become part of our freshly minted community.



 

Monday, September 9, 2019

WASU ABUBUWA DA BAKU SANI BA GAME DA MARIGAYI SHUGABA MUGABE



An haifi marigayin a ranar 21/2/1924 ya rasu 6/9/2019. Mugabe ya karbi ragamar shugabancin kasar Zimbabwe daga shekarar 1980 zuwa 1987. Daga nan ya kuma yi nasarar ɗarewa akan gadon shugabancin kasar daga 1987 har zuwa 2017.
Robert Mugabe ya auri matarshi ta farko Francesca yar asalin ƙasar Ghana, wadda ta rasu a shekarar 1992.
Mugabe shine shugaban kasa mafi ilimi a duniya don kuwa yana shaidar karatun digiri har guda bakwai sannan kuma yana da shaidar kammala digirin digirgir.

TUNA BAYA
Dan jarida: yallabai baka ganin ya dace kayi retire daga mukaminka na shugaban ƙasa a matsayinka na mai shekara 89
Mugabe: me ya hana ka yima sarauniyar England wannan tambaya ko kuwa sai yan Africa?
 
TUNA BAYA
Obama: ka amince da auren jinsi daya a kasarka.
Mugabe: ka fara aurena sannan na amince

TUNA BAYA
1- Idan kana shan taba kuma budurwarka ma tana sha to sunan soyayyarku ''Operation fire for fire''
2- Babu abinda yafi haushi irin abokin fadanka ya sambada maka mari, a raba ku baka rama ba.
3- Mata sun fi maza kwadayin jima'i shine dalilin da yasa Allah ya sanya masu al'ada don su rika huatawa

Thursday, September 5, 2019

AN ƘARA ƘONA JIRGIN SOUTH AFRICA NA BIYU A ƘASAR ZAMBIA.



Kasashen Africa na cigaba da Allah wadarai da halin dabbobi wanda wasu daga cikin matasan ƙasar South Africa suka ƙaddamar ga yan asalin ƙasar Nigeria mazauna ƙasar.

Matasan dai suna cigaba da kashe-kashen rashin imani ga mazauna ƙasar yan asalin wasu kasashe musamman Nigeria.

A cewar maharan wai yan ci ranin sun yi yawa kuma sun kai matsayin samun abin rufin asiri a ƙasar alhali su yan asalin ƙasar suna fama da matsalar kashe wando.

Sun manta network mafi girma a Nigeria wato MTN, da DSTV da shop rite dss duk mallakin ƙasar Afirika ta Kudu ne. Amma wannan bai sanya yan Nigeria sun dauki makami akansu ba.

Cigaba da kisan gillar ga yan Nigeria ya sanya wasu jahohi zanga zangar nuna kin jinin duk wata alaka tsakanin Nigeria da South Africa.


BARBARA TRUMESLEK MATASHIYAR DA TA AURI KARE A KASAR NORWAY


Wata matashiya mai kimanin shekaru 23, ta shiga dakin amarci da sabon angonta wato Rudolf. Barbara ta bayyana yadda ta hadu da angon nata a wata matattarar dabbobi dake kasar ta Norway. Hakanan kuma ta bayyana cewa akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakaninta da mijin nata.

Da ƴan jaridu suka tambaye ta game da alakar jima'i a tsakanin su, sai ta kada baki tace "alakar jima'i abu ne na sirri da ba zata iya bayyanawa duniya ba, amma dai ko ma menene mijin nata yana iya kokarinsa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na mai gidanta"

Auren Barbara da Rudolf dai ya biyo bayan halatta aure tsakanin mutum da dabbobin gida (Zooconractual union) wanda kasar ta Norway tayi. Sai dai dokar ta sanya takunkumi ga auren dabbobin daji da na ruwa.

Monday, August 19, 2019

WANI MUTUM YA WATSAWA MATARSA DA ƳAƳANSA ACID A KATSINA


Wani mutum wanda har yanzu ba'a tabbatar da sunansa ba ya watsawa matarsa da ƴaƴansa acid a lokacin da suke bacci.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ɗandume dake jahar Katsina.

Mutumin dai ma'aikaci ne a Union Bank reshen karamar hukumar dake jahar. Har ya zuwa yanzu dai ba'a san dalilin mutumin na aikata wannan danyen aiki ba.

Yanzu haka dai ba'a san inda mutumin ya ɓuya ba, sai dai Rabi wato matar da ƴaƴan nasa an garzaya dasu zuwa asibitin koyarwa ta Jami'ar Ahmadu Bello dake shika don ceto rayuwar su.