Thursday, September 5, 2019

AN ƘARA ƘONA JIRGIN SOUTH AFRICA NA BIYU A ƘASAR ZAMBIA.



Kasashen Africa na cigaba da Allah wadarai da halin dabbobi wanda wasu daga cikin matasan ƙasar South Africa suka ƙaddamar ga yan asalin ƙasar Nigeria mazauna ƙasar.

Matasan dai suna cigaba da kashe-kashen rashin imani ga mazauna ƙasar yan asalin wasu kasashe musamman Nigeria.

A cewar maharan wai yan ci ranin sun yi yawa kuma sun kai matsayin samun abin rufin asiri a ƙasar alhali su yan asalin ƙasar suna fama da matsalar kashe wando.

Sun manta network mafi girma a Nigeria wato MTN, da DSTV da shop rite dss duk mallakin ƙasar Afirika ta Kudu ne. Amma wannan bai sanya yan Nigeria sun dauki makami akansu ba.

Cigaba da kisan gillar ga yan Nigeria ya sanya wasu jahohi zanga zangar nuna kin jinin duk wata alaka tsakanin Nigeria da South Africa.


Previous Post
Next Post
Related Posts

0 comments: